Girgizar kasa ta rusa gidaje sama da 100 a Indonesiya
May 23, 2025Girgizar kasa da ta afkawa tsibirin Sumatra na kasar Indonesia mai karfin maki 5.7 a ma'aunin Richter a wannan Juma'a, ta rusa gidaje 140, to sai dai babu rahoton asarar rai zuwa yanzu.
Karin bayani:Fashewar wani dutse mai aman wuta ya yi sanadin rayuka a Indonesiya
Mai magana da yawun hukumar kula da yanayi ta kasar Abdul Muhari, ya shaida wa manema labarai cewa karfin girgizar kasar ya karu a wasu yankunan kasar. Sai dai babu alamar afkuwar ibtila'in motsin igiyar ruwa ta tsunami.
Karin bayani:An rantsar da sabon shugaban Indonesia Prabowo Subianto
A shekarar 2004 annobar igiyar ruwan tsunami ta halaka mutane sama da dubu dari da saba'in a Indonesiya, sai kuma a cikin watan Janairun shekarar 2021 da girgizar kasa ta halaka mutane sama da 100, tare da raba dubbai da gidajensu, yayin da a shekarar 2018 igiyar ruwan tsunami ta yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu biyu da dari biyu.