Ghana za ta ci moriya daga Indiya a fannoni da dama
July 3, 2025Dangantaka tsakanin Ghana da Indiya ta samo asali ne a zamanin shugaban Ghana na farko Dr. Kwame Nkrumah, a karkashin kungiyar 'yan ba ruwanmu, kafin ta rikide zuwa dangantakar tattalin arziki da ci-gaban kasa. Dama dai, Indiya na daukar Ghana a matsayin tabbatacciyar dimukuradiyya, kuma kasa mai tasowa a fannin tattalin arziki.
Ababen da Ghana ta ci moriya daga Indiya
Ministan harkokin Wajen Ghana, Samuel Okudzeto Ablakwa, ya ce kasashen biyu na sa ran samun sakamako mai karfi ta fuskar kasuwanci da ababen more rayuwa. Dama dai. Indiya ta ba da goyon bayanta wajen gina babbar fadar gwamnatin Ghana, tare da kafa cibiyar Ghana-Indiya Kofi Annan a ICT. Sannan, Indiya na tsayuwar daka ga ci-aban Ghana, inda ta bayar da tallafin samar da layin dogo na zamani na Tema zuwa Mpakadan.
Karin bayani:Matakin Indiya ya shafi Afirka
Minista Okudzeto Ablakwa, ya ce : "Mun ji dadii da firayiminista Modi ya zabi Ghana a matsayin kasa ta farko da ya ziyarta a rangadin kasashe biyar , yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa taron koli na BRICS. Indiya ta kasance a shekaru da dama amintacciyar aminiya. "
Ci-gaban da ziyarar Modi za ta haifar a Ghana
Cinikayya tsakanin kasashen biyu ta samu ci-gaba a cikin 'yan shekarun nan, inda jarin da Indiya ta zuba a Ghana ya kai sama da Dalar Amurka biliyan uku a masana'antu magunguna, da fannin noma, da makamashin da ake sabuntawa. Hasali ma, an rattaba hannu kan wasu yarjeniyoyi da dama tare da kaddamar da wasu tsare-tsare na hadin gwiwa da nufin karfafa alaka a fannin diflomasiyya da kasuwanci da al'adu da kuma fannin kiwon lafiya.
John Mahama ya karrama Narendra Modi
Firayiministan Indiya, Narendra Modi, ya samu lambar girmamawa mafi girma ta kasar Ghana yayin ziyararsa ta kwanaki biyu. Wannan, shi ne karon farko da wani shugaban Indiya ya kai ziyara a kasar Ghana cikin shekaru 30. Saboda haka ne fadar mulki ta Accra ta shirya liyafa ta musamman, inda Shugaba John Dramani Mahama ya ba wa Firayimminista Narendra Modi daya daga cikin muhimman lamba ta kasar.
Karin bayani: Indiya na dari-dari da karin kasashe a BRICS
Shugaba Mahama, ya ce: "Wannan karramawar, alama ce ta kara dankon zumunci na ci-gaba da aiki domin karfafa zumuntar Indiya da Ghana. Indiya za ta ci gaba da tsaya wa mutanen Ghana, kuma ta ci gaba da bayar da gudunmawa a matsayin aboki na gaskiya kuma abokin ci-gaba."
Karin bayani: John Mahama na nazarin habaka arzikin kasa a Ghana
Gabanin ficewarsa zuwa kasar Trinidad da Tabago, Firministan Narendra Modi ya yi jawabi a majalisar dokokin kasar Ghana, inda ya yaba da jajircewar kasar wajen kare darajar dimukuradiyya, yana mai bayyana kasar a matsayin “haske ga dukkan nahiyar Afirka."
Ya ce: " Idan muka duba Ghana, muna ganewa cewar kasa ce da ke haskakawa da karfin gwiwa, kuma ta canza kalubale zuwa fasaha da kyawawan halaye."