Rage kudin aikin Hajji a Ghana
February 6, 2025Farashin Hajjin na dala $4,130, wanda shine mafi karanci a firashen Hajji na dala $5, 000 a yankin. Rangwamin da aka samu wani mataki mataki ne da zai kara fadada yawan adadin al'umma maniyyata. Sai dai kamin isowa wannan gabar ko yaya lamura suke wannan dai muryar Hon. Collins Dauda kenan, jagoran kwamitin aikin Hajjin inda yake bayyana gagarumin rangwami a bana a firashen Hajji na shekarar 2025.
Karin Bayani: Zargin cin hanci a tantance ministocin Ghana
Bisa ga shawarar shugaban kasa an tsaida firashen Hajjin shekarar 2025 kan kudin sidi Ghc62,000 wanda kwatanci ne na dalan Amurka $4,130, kan canjin kowane dala 1 a sidi 15. Sanin kowa ne cewar canjin kudi sau tari kan kasance da rahusa a kasuwannin bayan fage idan an kwatanta da banki.
Farashin hajjin a bana na dala 4,130 wanda ya kumshi duk ziyarce-ziyarce, makwanci, abinci da duk sauran abubuwa, inda kuma jama'a ke ra'ayin cewa basu zaci firashen zai wuce sidi 50,000 ba. Sai dai abin da ke tayar da kura a yanzu shi ne zargin cewa tsohon kwamitin Hajjin, ya bar wa gwamnati ajiyar bashin kimanin dala miliyan $5.526.000.66, wanda kawo yanzu tsohon jagorancin ba su ce uffan ba tukuna.