Ghana ta kwace albashin ministoci kan kin bayyana kadarori
May 6, 2025Shugaba John Dramani Mahama na Ghana ya kwace albashin watanni uku na ministocinsa sama da 40 da sua ki bayyana kadarorinsu a matsayin tara, inda ya yi barazanar korarsu da zarar sun kai ranar Laraba 7 ga watan Mayu ba su bayyana ainihin abin da suka mallaka a duniya ba.
Karin bayani:China ta ce 'yan kasarta uku da aka sace a Ghana sun kubuta
Tun bayan rantsar da shi a zangon mulkinsa na biyu a cikin watan Janairun da ya gabata, shugaba Mahama ya ayyana dukiyar da ya mallaka, sannan ya umarci mukarrabansa su yi koyi da shi, kafin zuwa karshen watan Maris, ko kuma ya ci tarar su albashin watanni uku, sai kuma karin na wata daya a matsayin gudunmawa ga asusun tallafin kiwon lafiya mai suna Mahama Cares.
Karin bayani:Ghana: Shugaba Mahama ya nada ministoci 42
Wannan dai wani bangare ne na alkawarin da shugaban ya yi na yaki da cin hanci da rashawa da ya yi wa kasar katutu, wadda ke cikin halin matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa.