SiyasaAfirka
Ghana ta fara wani sabon yunkuri na dawo da AES cikin ECOWAS
April 23, 2025Talla
Sabon shugaban kasar Ghana John Mahama ya fara wani yunkuri na dawo da kasashen AES da suka hada da Mali, Burkina Faso da Nijar zuwa kungiyar ECOWAS tun bayan juyin mulki da aka yi a kasashen.Shugaban ya furta hakan ne a yayin bikin cika shekaru 50 da kafa kungiyar.
Karin bayani: Hafsoshin sojan ECOWAS na taro kan Nijar
Kafin sanar da daukar wannan mataki da shugaban na Ghana ya yi, takwaransa na Senagal Bassirou Diomaye Faye shi ne ya fara wannan yunkuri na dawo da kasashen na Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar cikin kungiyar amma abin ya ci tura.