Ghana: Shugaba Mahama ya nada ministoci 42
January 22, 2025Gwamnatin da ta shude ta jami'iyyar NPP ta yi aiki ne da ministoci sama da 120, abinda kuma ya kasance jigo a sakonnin neman zabe na sabon shugaban Ghana John Mahama, kuma ya ci galaba bisa alkawarin aiki tare da ministoci 60 kacal. Duk da cewa zabin wasu ministocin a wasu ma'aikatu ya janyo cece-kuce musamman ma zabin musulmi a matsayin jagoran hukumar kula da cacar lotto haka kuma samun akasi na wasu ministoci a wasu ma'aikatun, ko da yake manazarta ayyukan gwamnati na yaba daukacin ministocin da aka zaba da a cewarsu matasa ne, wadanda suka dace.
Sai dai su kansu matasan da ke tsokaci akan zabin wasu ministocin daga jihohinsu, a yankin Bole Bamboi na yankin Savanan jihar arewaci da kuma matasa na yankin Ho a jihar Oti, barazana suke yi ta gudanar da zanga-zanga kan rashin samun wakilicin dan asalin yankunansu. Amma kuma a jihar Ashanti inda aka zabi Mohammad Muntaka Mubarak a matsayin ministan tsaron cikin gida.
Yawan ministoci ko kuwa fadin gwamnati ta yi matukar tasiri a yawan sukar da gwamnatin da ta shude ta saba sha, na daga cikin dalilan da cin hanci da rashawa ya yi katutu, kuma ko shin rage yawan ministoci da kuma hade wasu ma'aikatun da gwamnatin ta fara yi kan iya kai ga cimma burin yakar rashawa da hukumomi a Ghana ke yi?