Ghana: Aiki da kirkirarriyar basira a fannin ilimi
July 24, 2025A yayin da Ghana ta fara gwajin amfani da kirkirarriyar basira da ake kira Artificial Intelligence ko kuwa AI, a fannin karatu musamman a jami'o'i, da kallonsa a matsayin wani sabon babi a fuskar ilimi wanda ke daukar hankalli sosai. Ana kuma gargadi da yin hattarar amfaninsa ga dalibai da malamai haka kuma da kare tsarin koyarwa nan gaba kasancewar ana amfani dashi daga tallafin rubuce-rubuce zuwa ga koyarwa ta zahiri. Farfesa Kofi Sarpong na tsangayar kimiyyar comfuta a jami'ar Ghana ya ce dalibai da dama na samaun hanya mafi sauki, saboda idan an basu ayyukan gida da AI ne suke yinsu.
A duk faɗin duniya fasahar AI na canza yadda ake koyarwa da koyo. Amma tare da duk wata sabuwar dama kan zo da nata ƙalubale, kuma yayin da alƙawarin AI ke tafe da damomi masu ban sha'awa, abubuwan da suka shafi ɗabi'a, bayanan sirri da kuma dogaro da AI fiye da kima abin damuwa ne. Farfesa Solomon Mensah jami'in gudanarwa a tsangayar kimiyyar comfuta na jami'ar Ghana ya ce.
"Wasu daliban na dogaron da ya wuce iyaka ga fasahar AI. Kila suna iya gabatar da ayyukan da aka basu na gwaji a lokaci tamkar da kansu ne suka yi amma kuma ba haka bane, wanda bai da kyau idan har an yi ne da AI. Zai fi dacewa idan ma za su rika karawa da ambaton inda suka kwakwalo amsa".
Dalibai sun rungumi kirkirarriyar basirar ta hanyoyin da yake amfanar da su daban-daban:
"Na kasance ina jinkiri wajen ayyukana da kuma bincike, na kan saura kan karance-karance ko kuwa ina saka tambaya a google kamin na kammala ayyuka na, amma tunda na gano AI, maudu'in kawai nake sakawa kuma sai na samu taikaitaccen amsa a dunkule, ta yadda nake samun fahimta a saukake haka da hanzarta nazari na".
Sai dai babbar tambayar ita ce shin Ghana ta shirya wajen jona AI a tsarin ilimi baki daya? Ga karin jawabin Prof Adu Sarpong.
"Ghana dai kan bata yi shiri ba saboda tsarin karatu da akwai yafi mayar da hankali ne kan haddacewa. Shi yasa yake zama babban kalubale a tunanin saka AI a tasrin ilimin kacokan."
Kazalika Prof. Sarpong ya yi bayanai a kan tambayar da'a a kimiyance, da wadanne irin bayanai na kansu ne dalibai ke sakarwa kana suna da kariyarsu, ina ake adana su, waye mamallaki kana shin za'a iya amincewa da tsarin AI? Domin duk da kasancewar AI wata basira mai karfi bata iya maye gurbin alakar dan adam ba, domin akwai amsoshi da dama wadanda AI ba zai iya samarwa ba.