Gaza: An mika wa Hamas sabon daftarin yarjejeniya
August 18, 2025Masu shiga tsakani kan yakin Gaza sun mika wa tawagar Hamas sabon daftarin yarjejeniyar tsagaita wuta a birnin Alkahira na Masar kamar yadda wata majiya mai kusanci da kungiyar ya tabbatar wa kamfanin dillacin labaran Faransa AFP.
Sabon daftarin yarjejeniyar ya sake fayyace shawarwarin da Amurka ta gabatar da suka shata tsagaita wuta na tsawon kwanaki 60 da kuma sakin ragowar 'yan Isra'ila da Hamas ta yi garkuwa da su a lakacin harin ranar bakwai ga watan Oktoba wanda ya haddasa yakin Gaza.
Majiyar ta kuma ce Hamas za ta nazarci wannan daftari da kasashen Masar da Qatar suka mika wa tawagarta karkashin jagorancin Khalil al-Hayya domin share fagen tsagaita wuta na dindindin a dan karamin yankin na Falasdinu.
A gefe guda ministan harkokin wajen Masar Badr Abdeletty ya shaidar da cewa a yanzu haka firaministan Qatar Mohammed ben Abdelrahmane Al-Thasi na a birnin Alkahira domin yin matsin lamaba ga bangarorin biyu don amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta.