Kusan shekara guda bayan da gwamnatin Najeriya ta amince da biyan naira 70,000 a matsayin mafi karancin albashi har kawo yanzu wasu jihohin kasar na jan kafa wajen aiwatar da wannan alkawari, yayin da ma'aikata ke ci gaba da dandana radadin tsadar rayuwa mai nasaba da hauhawar farashin kayan masarufi da kuma janye tallaffin man fetur. Mun tattauna da Aliyu Isa Aliyu da Khadijah Suleiman Saulawa.