Akalla Naira miliyan 150 da gidaje masu daki uku-uku da kuma lambar girmamawa ta OON ne kowacce daga cikin ‘yan tawagar kwallon kafar mata ta Najeriya, Super Falcons ta koma gida da su bayan lashe gasar cin kofin kwallon kafar Afirka ta mata ta 2025. Bakinmu na yau su ne Sharfaddeen Bature matashi a Najeriya da kuma Zainab Buba Galadima 'yar siyasa mai rajin kare hakkin mata.