A farkon wannan makon ne Shugaban Gwamnatin Mulkin Sojin Jamhuriyar Nijar Janar Abdourahmane Tiani ya yi wani furuci da ya ja hankalin 'yan kasar inda ya ce "Yanzu ba lokaci ne na yin gaba da juna ko kuma wata muguwar adawa marar amfani ba, illa kawai lokaci ne da ya kamata al'ummar kasar su yafe wa juna da kuma manta duk wani abin da ya faru a baya.