Yuwuwar kisan kare dangi a rikicin Sudan
June 23, 2025Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa ana iya fuskantar kisan kare dangi na kabilanci a rikicin da ke faruwa a kasar Sudan, inda ake fafatawa tsakanin sojojin gwamnati da mayakan kugiyar RSF.
Karin Bayani: Jaridun Jamus: Rikicin Najeriya d siyasar Burundi
Virginia Gamba maitaimakawa babban sakataare janar na Majalisar Dinkin Duniya ta ce duk bangarorin suna aikata ta'asa na yaki. Kuma ta ce yuwuwar aikata kisan kare dangi a rikicin na karuwa.
Tun shekara ta 2023 kasar Sudan ta fada cikin yakin basasa tsakanin sojojin gwamnati karkashin Shugaba gwamnatin mulki soja Janar Abdel Fattah al-Burhan, da jagoran kungiyar RSF, Mohamed Hamdan Daglo. Dubban mutane suka mutu sakamakon wannan rikici, yayin da fiye da mutane milyan 13 suka tsere daga gidajensu.