Gargadin tsunami a Rasha da Japan da kuma Amurka
July 30, 2025Talla
Hukumar binciken yanayin ta Amurka ta ce girgizar kasar na da karfin maki 8.8 bisa ma'aunin richter da kuma zurfin kilomita 19.3, lamarin da ya sa gargadi kan matsalar da za ta haifar. A faifain bidiyon da ya wallafa a shafinsa na Telegram, gwamnan Kamchatka Vladmir Solodov, ya ce girgizar kasa ta yi muni kuma ta kasance mafi karfi a cikin gomman shekaru.
Karin bayani: Shekaru 15 da bala'in Tsunami
A yanzu haka dai, an fara gargadin mazauna yankunan da ke cikin hatsarin a tsibirin Hawaii da su kaurace wa matsugunansu. Magajin garin arewacin tsibiran Kuril ya ce a safiyar ranar Larabar, an kwashe mutane da dama sakamakon ambaliyar ruwa da ta wanke gidaje da dama.