Gargadin Amirka game da yiwuwar fuskantar hare-hare a Abuja
November 7, 2011Al'ummomin yankin Arewa maso gabashin Najeriya sun bukaci Shugaba Goodluck Jonathan ya sauka daga mulki tunda ya kasa magance matsaloin tsaro a kasar.
A ‘yan lokutan nan dai yankin Arewa maso gabashin Najeriya shine ya fi kowane yankin fama da tashe-tashen hankula sanadiyyar hare-haren Bama-bamai da Kungiyar Jama'atu Ahlis Sunna Lidda'awati Wal Jihad, da aka fi sani da suna, Boko Haram ke ikirarin kaiwa.
Wannan yasa al'ummar yankin zargin shugaban Najeriya Goodluck Ebele Jonathan da halin ko oho da yankin ganin ya kasa magance abubuwan dake faruwa kuma har ya zuwa yanzu bai taba zuwa na musamman ganewa idonsa irin ta'adi da wannan hare-hare suka yi ba.
Saboda haka ne ma ya sa suka nemi shugaban ya yi murabus tunda kasa shawo kan matsalolin tsaro da ke rataye a wuyan sa kamar yadda Hon Yusuf Haruna daya daga cikin masu neman shugaban ya sauka ya shaida min.
Sun kuma zargi shugaban da kasa aiwatar da rahoton kwamitin da ya kafa karkashin jagorancin Ambassador Usman Gaji Galtimari wanda ya bashi shawara kan yadda ya kamata yayi don shawo kan matsalar tsaron musamman a yankin Arewa maso gabashin kasar.
Alhaji Yakubu Abdu Mairiga da Malam Bala Kali Gaya wasu mazauna yankin Arewa maso gabashin Najeriya sun bayyana min ra'ayoyin su kan halin da ake ciki dangane da tsaro a yankin dama Najeriya baki daya.
Sai dai wasu na ganin ba anan matsalar ta ke ba, su a ganin su kamata yayi a koma ga Allah domin neman saukin wannan matsala ta hanyar yin addu'o'i da Azumi a cewar su shine kawai ya saurawa talaka Najeriya.
Wasu kuma, kamar Malam Usman Gurama Malami a Babban Kwalejin Horar da Malamai ta gwamnatin tarayya dake Gombe na ganin zama a teburin shawara da masu gwagwarmayar shine kawai mafita ba amfani da karfi ko hanya ta murkushe rikicin ba.
Duk da cewa kura ta lafa harkoki sun fara komawa yadda suke a biranen Maidudguri da damaturu inda aka kai munanan hare-hare a karshen makon nan da ya hallaka mutane sama da dari jama'a na cikin fargaba da zullumi don kuwa ko da jiya sai da wasu mahara suka hallaka wani babban jami'in ‘yan Sanda da a Maiduguri bayan tasowa daga sallar Idi.
Sai dai Jami'an tsaro na gudanar da bincike kwakwab ga ababan hawa a cikin biranen dama jihohi makobta.
Mawallafi: Al Amin Suleiman
Edita: Umaru Aliyu