Ghana: Gargadi ga masu ikirarin karbar wahayi
August 13, 2025Ofishin kula da addinan na fadar shugaban kasar Ghana, ya bukaci irin wadannan malamai su rika mika sakonnin ga ofishin kula da sha'anin addinai domin a tantance a dauki matakai kafin su sanar wa al'umma. Gwamnati ta dauki matakin ne, domin aika gargadi ga masu ikirarin samun sakonnin wahayi daga Allah wadanda ke da alaka da jami'an gwamnati. Gwamnati ta ce hakan na kasancewa barazana ga tsaron kasa da kuma zaman lafiyar al’umma, biyo bayan wasu hotunan bidiyo da suka karade shafukan sada zumunta a kasar da ake ta tafka muhawara akansu. Wasu limaman kiristoci sun yi ikirarin ganin wahayin hadarin jirgin sama mai saukar ungulu da ya halaka jami’an gwamnati takwas a makon da ya gabata, kafin ma afkuwar al'amarin.
Wani limamin coci a birnin Accra Pastor Felix Nze ya yaba da matakin da gwamnati ta dauka, wanda a cewarsa hakan zai tsabtace sha'anin addinai daga batanci da zarce iyakokin da bai kamata a ce an keta ba. A yayin da gwamnati ke ci gaba da iya kokarinta a hukumance, haka daga fuskar tsaro ana ganin kiyaye maimaicin wannan ibtila'in. Sai dai wannan da'awar wahayi ba a Ghana kadai ake yin ta ba, har ma a wasu kasashen Afika ana fama da wannan. Hakan dai na haifar da ayar tambaya, ta shin gaskiya ne ko kuwa karairayi ne da alumma ke bukatar fadakarwa a kansu?