Zanga zangar kungiyar kwadago a Najeriya
July 27, 2022A wani yunkuri na kara matsin lamba ga gwamnati Najeriya a bisa neman kai karshen yajin aikin kungiyar malaman jami'o'i, dubban 'ya'yan kungiyar kwadagon kasar ta NLC sun bi sahun malaman da sauran jama'ar gari wajen wani gangamin da ke zaman irinsa mafi dauka na hankali a watanni biyar na yajin aikin ASUU.
An gudanar da zanga-zangar a Abuja babban birnin kasar, inda 'ya'yan kungiyar kwadagon Najeriya ta NLC ke jagorantar wata zanga-zangar neman matsi lamba ga gwamnatin kasar na kare yajin aiki na malamai na jami'o'i na kasar.
NLC dai ta ce, ta yanke shawarar tsunduma hannu da kafa ne bayan kallo daga nesa na tsawon watanni guda biyar daga nesa, ba tare da nuna alamun shawo kan rikicin da ke barazana ga karatu a jami'o'i na kasar ba.
Ayuba Waba shi ne shugaban kungiyar kwadagon kasar NLC kuma jagoran zanga-zangar da ta kai ga tsayawar lamura a harabar majalisun kasar guda biyu.
''Naira triliyan guda da doriya ne dai malamai na jami'o'in suke fadi suna da bukata a cikin neman hanyar sake raya harkar ilimin da ke lalacewa kuma ke kallon hijirar 'ya'yan manya zuwa kasashe na waje.
Dalar Amurka miliyan 357 ne dai babban banki na kasar ya ce, mahukunta na kasar sun bayar a cikin watanni uku da suka gabata da nufin tura 'yan kasar zuwa kasashen wajen a cikin neman samar da karatu mai inganci bayan rushewar lamura a jami'o'in kasar.
Kuma duk da korafin rashin kudi na biyan bukatar ASUU a fadar Sanata Shehu Sani da ke zaman tsohon dan majalisar dattawa ta kasar kuma daya a cikin masu taka rawa a zanga-zangar mai tasiri, akwai alamu na yaudara a bangaren mahukuntan da ke da kudade na tallafin man fetur amma kuma ke neman gaza tallafawa harkar ilimi cikin kasar''
Sabon matakin da ke zuwa a yayin da fage na siyasa ta kasar ke dada zafi dai daga dukkan alamu na neman rikidewa ya zuwa batu na siyasa ta kasar mai zafi.
Sannu a hankali yajin aikin na neman komawa zuwa makamin yaki a bangare na masu adawar da ke fadin masu tsintsiyar sun kasa ga batun ilimin.
Ana dai cigaba da yada wani faifan bidiyo na shugaban kasar da ke zargin 'yan mulkin baya da kasa ceto ilimi na jami'i na kasar.
To sai dai kuma a fadar farfesa Nasir Fagge da ke zaman tsohon shugaba na kungiya ta jami'o'i na kasar babu ruwa na kungiyar da siyasar da ke gudana a kasar yanzu haka.
Zanga-zangar, a fada ta masu kwadago na zaman matakin farko a cikin wani jeri na matakai na masu kwadagon da nufin matsin lambar mahukuntan.
ASUU ta ce tana shirin tafiya yajin aiki in har masu mulkin na Abuja suka kasa shawo kan matsalar.