Shirye-shiryen zaben Kanada
April 25, 2025Ana gangamin karshen na yakin neman zaben kasar Kanada wanda za a gudanar ranar Litinin mai zuwa 28 ga wannan wata na Afrilu, inda kuri'ar sanin ra'ayin masu zabe ta nuna cewa Firaminista Mark Carney na jam'iyyar Liberal mai ra'ayin gaba-dai gaba-dai ke kan gaba na yuwuwar lashe zabe, inda ya yi tazara wa babbar jam'iyyar adawa ta Conservatives ta masu ra'ayin mazan jiya da Pierre Poilievre yake jagoranci.
Karin Bayani: Ana zaben sabon shugaban jam'iyyar mai mulkin Kanada
Zaben na Kanada na zuwa lokacin da kasar take fito na fito da Amurka kan tsarin harajin kudin fito na kuma matakin Shugaba Donald Trump na Amurka cewa yana son mayar da Kanada ta zama jiha ta 51 ta Amurka, abin da ya harzika galibin 'yan kasar.
Ita dai kasar Kanada tana daya daga cikin manyan kasashe na duniya masu karfin arzikin masana'antu.