Gangamin adawa da yakin Isra'ila a Gaza a Muritaniya
April 7, 2025Talla
Masu aiko da rahotanni sun ce zanga-zangar da hadin gwiwar kungiyoyin fararen hula da na daliban jami'o'i suka shirya ta samu karbuwa, inda galibin makarantun gwamnati da masu zaman kansu suka kasance a rufe, kazalika harkokin kasuwanci da na sufuri sun takaita a wannan rana.
Masu boren sun yi ta nuna allunan da ke sukar matakin gwamnatin Isra'ila na sake kai hari a zirin Gaza tare da nuna fata na ganin an tsagaita buda wuta.
Wannan ce dai zanga-zanga mafi girma da masu adawa da yakin na Isra'ila suka shirya a kasar Mauritaniyya, tun bayan da bangarorin biyu na Hamas da Isra'ila suka fara bata-kashi a farkon watan Oktoban 2023.