Ganawar ministocin gida na ƙasashen Turai
June 10, 2011A yayinda ministan cikin gida na Jamus Hans-Peter Friedrich ke tattare da ra'ayin cewar wajibi ne a tinkari matsalar daga tushenta, hukumar zartaswa ta ƙungiyar tarayyar Turai ta ba da shawarar bin wata manufa ce bai ɗaya tsakanin ƙasashen ƙungiyar.
A dai halin da ake ciki yanzun babu wata alamar dake yin nuni da samun kusantar juna domin bin wata manufa bai ɗaya tsakanin ƙasashen ƙungiyar tarayyar Turai dangane da tsarin ba da mafakar siyasa. An yi tsawon shekaru da dama ana fama da kwane-kwane a shawarwarin da ake yi tsakanin ƙasashen. Ita kanta shawarar baya-bayan nan da kantomar ƙungiyar a al'amuran cikin gida Cecilia Malmström ta bayar, ga alamu ba ta samu cikakken goyan baya ba. Sakataren gida na ƙasar Belgium Melchoir Wathelet ya fito fili ya nuna takaicinsa game da lamarin:
"Duk kowa sai magana yake ta fatar baki na cewar wajibi ne mu yi hoɓɓasa. Amma bai kamata lamarin ya tsaya a nan ba tilas ne mu cimma wata manufa nan da shekara ta 2012."
Amma a nasa ɓangaren ministan cikin gida na Jamus Hans-Peter Friedrich gani yake cewar wajibi ne a tinkari matsalar 'yan gudun hijirar daga tushenta. Wajibi ne a magance ainihin abubuwan dake haifar da guje-gujen hijirar:
"Abu mafi muhimmanci shi ne samar da kwanciyar hankali a waɗannan ƙasashe. Hakan ita ce zata taimaka a samu ci gaba a shekaru masu zuwa. Wajibi ne mu taimaka wajen ba da kyakkyawan haske ga makomar al'uma a waɗannan ƙasashe."
Wannan ra'ayin dai hatta magabatan Hans-Peter Friedrich suna ɗauke da shi. Sai dai banbancin dake akwai shi ne sabon mawuyacin halin da aka shiga a arewacin Afirka dake ƙara haddasa guje-gujen hijira. Kafin ɓillar juyin-juya-halin a ƙasashen kudancin tekun baharrum, gwamnatocin ƙasashen na taimakawa wajen hana tuttuɗowar 'yan gudun hijira da baƙin haure zuwa nahiyar Turai. Amma a yanzu al'amura sun canza suka ɗauki wani sabon salo. A mayar da martani akan haka ƙasashen na Turai suka fara shawarar ƙara ƙarfafa matakan tsaro akan iyakokinsu. Ga dai abin da kantomar ƙungiyar tarayyar Turai akan manufofin cikin gida Cecilia Malmström take cewa domin kwantarwa da masu sukan lamirin wannan mataki hankalinsu:
"Hakan ba ya nufin kawo ƙarshen yarjejeniyar Schengen. Abin da ake ƙoƙarin yi shi ne ba da cikakkiyar kariya ga wannan manufa, saboda yarjejeniyar ta Schengen wata gagarumar nasara ce ga ƙasashen Turai."
Musamman ƙananan ƙasashe na ƙungiyar na nuna ɓacin ransu game da neman taƙaita tafiye-tafiye da ake ga wasu ɗaiɗaikun mutane. Ministar cikin gida ta ƙasar Ostriya Johanna Mikl-Leitner ma nuna fargabarta tayi game da cewar wasu ƙasashen zasu nemi yin amfani da matakin ƙayyade shige-da-ficen saboda wasu dalilai na manufofin cikin gida, kamar dai yadda lamarin ya kasance dangane da ƙasar Denemark, wadda ake zarginta da ɗaukar wannan mataki don neman suna tsakanin al'umarta.
Mawallafi: Peter Heilbrunner/Ahmad Tijani Lawal
Edita: Umaru Aliyu