SiyasaJamus
Friedrich Merz zai gana da Zelensky a Berlin
May 28, 2025Talla
Sugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz, zai karbi bakuncin Shugaban Kasar Ukraine Volodymyr Zelensky a yau Laraba.
Ziyarar za ta mayar da hankali ne kan tallafin Jamus ga Ukraine da kokarin cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da Rasha, in ji kakakin gwamnatin Jamus Stefan Kornelius a cikin wata sanarwar gwamnatin da ya bayyana.