SiyasaChadi
Fursunoni dari sun tsere daga wani gidan yari a Chadi
April 19, 2025Talla
Lamarin ya yi sanadin mutuwar akalla mutane uku, kamar yadda majiyoyin tsaro suka rawaito.Majiyoyin sun shaida Cewar fursunonin na kokawa ne da rashin samun isashen abinci.
Gidan Kurkukun da ke da nisan kilomita biyar daga gabashin garin Mongo da ke a tsakiyar Chadin, da aka gina tun shekaru goma da suka wuce ya kasance gidan yari mafi tsaro a Chadin.