Fubara zai kalubalanci matakin dakatar da shi a kotu
March 19, 2025A cikin wata sanarwa da ya fitar, gwamnan jihar Rivers da aka dakatar Siminalayi Fubara ya bayanna irin matakai da ya dauka tun bayan hawansa mulki zuwa lokacin da aka dakatar da shi, inda ya ce ya yi kokarin kare rayuka da dukiyoyin al'umma da kuma kawo ci-gaba a jihar. Sai dai wasu 'yan majalisar dokokin jihar da ke adawa da mulkinsa sun ta kawo cikas ga yunkurin da ya yi na daidaita sabanin da ke tsakaninsu. Sannan Fubara ya ce babu makawa, zai tuntubi duk wadanda suka dace wajen shigar da kara a kotu don ta tabbatar da dorewar mulkin dimukuradiyyar a jihar Rivers.
Jami'an tsaro sun mamaye gidan gwamnatin jihar Rivers bayan dakatar da Siminalayi Fubara da shugaban Najeriya ya yi a cikin dokar ta-bacin da ya kakaba. An tabbatar da cewar Fubara ya fita daga gidan gwamnatin Rivers, kuma ana dakon isowar Kantoma da zai rike jihar cikin watanni shida, lamarin da ya sa jama'a fadawa cikin zullumi.
'Yan PDP sun nemi Tinubu ya lashe amansa kan Rivers
Majalisar dattawan Najeriya ta dan jinkirta tattaunawa kan kudirin dokar ta-baci a Rivers a zamansu na safiyar Laraba (19.03.2025) game da amincewa koko a'a da dokar. Sai dai tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya kuma jigo a am'iyyar PDP mai adawa, Atiku Abubakar ya bayyana matakin da shugaba Bola Tinubu ya dauka a jihar Rivers a matsayin haramtacce. Su ma gwamnonin jam'iyyar PDP a Najeriya sun nemi Shugaba Bola Tinubu ya lashe amansa kan dakatar da gwamnan Rivers Siminalayi Fubara da ya yi.
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya sanar da kafa dokar ta-baci a jihar Rivers da ta yi ta fama da rikicin siyasa kusan shekaru biyu, inda kuma tuni ya sanar da sauke gwamna Siminalayi Fubara na wucin gadin watanni shida tare da nada wani tsohon soja a matsayin kantoma. Shugaban na Najeriya Bola Tinubu a jawabin da ya yi wa 'yan kasa a yammacin Talata kan aza dokar ta-bacin ya zayyana laifukan Gwamna Fubara da suka hada da rushe ginin majalisar jahar da ya yi a baya ba tare da gyara ta ba, yana mai bayyana takaicin kan yadda duk da kokarin shiga tsakani a rikicin siyasar da ya yi ya ce bangarorin biyu sun ta yin biris da yarjeniyoyi da aka riga aka cimmawa.
Lauyoyi suka ce dakatar da Fubara ya saba wa doka
Kungiyar Lauyoyin Najeriya NBA ta ce kafa dokar ta baci da shugaban kasa ya yi a jihar Rivers da kuma dakatar da gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa da 'yan majalisar dokokin jihar na watanni shida, ya saba wa kundin tsarin mulkin tarayyar Najeriya. Amma rahotannin da ke zuwa daga birnin Port Harcourt, sun nunar da cewar kantoman rikon kwarya na Rivers Vice Admiral Ibok-Ete Ibas ya isa fadar shugaban kasa don tattaunawa da Bola Ahmed Tinubu.
Karin bayani: Jam'iyyar PdP ta Najeriya na cikin rudani
Tuni kuma shugaban ya sanar da dakatar da Gwamna Fubara na wucin gadin watanni shidda, tare da nada wani tsohon Sojin Ruwa Vice Admiral Ibokette Ibas mai ritaya wadda dan yankin na Niger Delta ne domin ya rike jihar na tsawon watannin shida.
Bayan wannan sanarwa, jami'an tsaron soji suka dira a gidan gwamnatin jihar ta Rivers tare da yi wa daukacin gidan kawanya da kuma tare duk wata hanya gaba da baya da ke kai wa zuwa gidan gwamnatin da ke Fatakwal, babban birnin jihar.