SiyasaGabas ta Tsakiya
Fiye da mutum 1000 suka rasu a rikicin Siriya
July 21, 2025Talla
Tashe-tashen hankali na bangaranci a kudancin Siriya ya halaka fiye da mutane 1,260 kafin aiwatar da yarjejeniyar tsagaita wuta ta baya-bayan nan.
Wata kungiyar da ke sa ido kan yake-yake ce ta fadi hakan a ranar Litinin a yayin da take ci gaba da tattara alkaluma.
Siriya ta zargi Isra'ila da jefa kasar cikin yaki
Mutanen da suka mutu a rikicin da ya faru a lardin Sweida sun hada da mayakan Druze guda 505 da fararen hular Druze din 298.
Sauran sun hada da jami’an tsaron gwamnati guda 408 da 'yan kabilar Sunni Bedouin 35.
An ayyana tsagaita wuta a rikicin yankin kudancin Siriya
Har ila yau, akwai kuma sojojin gwamnati 15 da Isra’ila ta kashe a hare-harenta kan Siriya in ji kungiyar.