Firaministan Kanada na iya yin murabus saboda shan matsi
January 6, 2025Firamintan Kanada Justin Trudeau da ke fuskantar matsin lamba a makonnin da suka gabata na iya mika takardar yin murabus dinsa a kwanaki masu zuwa, kamar yadda jaridar kasar The Globe and Mail ta ruwaita a daren jiya Lahadi.
Jaridar ta ambato wasu majiyoyi guda uku da ke da ruwa da tsaki a harkokin gwamnati mai ci, wanda suka tsegumta mata cewa firaministan na iya jefar da kwallon mangaro tun daga wannan Litinin.
Mataimakiyar firaminista kana ministar kudin Kanada ta ajiye aiki
Wannan lamari dai na da nasaba da rikincin siyasa da ya barke a Kanada bayan murabus din mataimakiyar firaministan saboda rashin fahimtar juna a kan yadda Justin Trudeau ke tafiyar da manufofin tattalin arzikin kasar a cikin yanayi na hamayya da Amurka da kuma barazanar Donald Trump na kara mata haraji kan kayan da shigar wa.
Wannan lamari ne ma dai ya rage farin jinin firaministan a idanuwan 'yan Kanada tare da zarginsa da jefa kasar cikin yanayin matsi da tsadar rayuwa.