Firaministan Japan ya rasa rinjaye a majalisa
July 21, 2025A zaben sabunta wa'adin kujeru 125 daga cikin 248 na 'yan majalisar dattawa ta Japan da aka gudanar a ranar Lahadi jam'iyyar Shigeru Ishiba LDP ta masu ra'ayin mazan jiya da abokiyar kawancenta sun tashi da kujeru 47 kacal yayin da jam'iyyar masu tsattsauran ra'ayi da kyamar baki ta samu gagarumar nasara kamar yadda sakamakon da aka fitar a Litinin din nan ya nunar.
Karin bayani: Jam'iyya mai mulki ta gaza samun rinjaye a zaben Japan
Wannan lamari ya jefa Japan a cikin wani irin yayayin siyasa da ba a taba shiga cikin irinsa ba tun bayan yakin duniya na biyu inda gwamnati mai ci ke rasa rinjaye a majalisun kasar guda biyu masu tasiri.
A yanzu dai kallo ya koma kan makomar firaminsta Shigeru Ishiba da farin jininsa ke kara disashewa a idanuwan 'yan Japan saboda tsadar rayuwa da kuma tagomashi da jam'iyyar masu tsattsauran ra'ayi ke samu.