Firaministan Isra'ila da kotun ICC ke nema ya isa Hungary
April 3, 2025Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya isa kasar Hungary a wannan Alhamis, don amsa gayyatar takwaransa na kasar Viktor Orbán, ziyararsa ta farko kenan zuwa Turai tun bayan da kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ICC ta ba da sammacin kama shi, kan aikata laifukan yaki da cin zarafin bil'adama a Gaza.
Karin bayani:Netanyahu ya yi watsi da sammacin kotun ICC
Fadar firaministan Isra'ila ta ce Mr Netanyahu zai gana da Viktor Orbán da kuma shugaban Hungary Tamás Sulyok, kuma zai koma gida ranar Lahadi mai zuwa bayan kammala ziyarar.
Hungary na cikin kasashen duniya da suka amince da kotun ICC, to amma ta ba shi tabbacin ba za ta kama shi ta mika wa ICC ba.
Karin bayani:Hungary ta zargi Turai da yin kafar ungulu a yakin Ukraine
Mr Orban ya aike da gayyatar ga Mr Netanyahu, jim kadan bayan da kotun ta ICC ta ba da izninin kama shi.