Maradi: Fata ga Bishop Ingnatius Anipu
June 3, 2025Babban burin Monsignor Ingnatius Anipu shi ne, hada kan mabiya da koyarwa ta bushara cikin adalci.
Bikin nadin nasa dai, ya samu halartar manyan shugabannin addinin Kirista na kasar ta Nijar da na kasashe makwabta ciki har da gwamnan jihar ta Maradi da Sultan na Maradi da Sultan na Gobir.
Bishop Ingnatius Anipu dai ya canji takwaransa dan kasar Burkina Faso, kuma kafin nadin nasa ya rike mukamai da dama a Nijar da sauran kasashe.
Saboda kwarewarsa a harkar zamantakewa ne ma, ake ganin zai taka rawar gani wajen tabbatar da zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai dabam-dabam a kasar kamar yadda Fasto Lawali Abdou sakataren kungiyar CDIR ya shaidawa DW.
Shi ma da yake karin haske kan nadin sabon Bishop din, shugaban kungiyar hadin kan Musulmi da Kirista ta CDIR Cheik Malam Tukur ya nunar da cewa tabbas Bishiop Anipu zai bayar da muhimmiyar gudunmawa wajen kara samun fahimhar juna tsakanin al'umma a yankin.