Fashewar nakiya ta kashe mutane a jihar Borno
April 13, 2025Mutanen yankin dai na zargin kungiyar 'yan ta'addan Boko Haram da kai harin a wani bangare na sabon yunkurin da take yi na sake dawowa da karfinta a jihar Borno.
Gwamnan Jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya tabbatar da lamarin, yana mai cewa ''mun samu rahoton abin da ya faru, kuma ina da yakinin cewa za a iya shawo kan wannan matsala. Za mu ci gaba da karfafa gwiwar al'umma, kuma ba za mu bari wannan al'amari ya hana zirga-zirga tsakanin Maiduguri da Damboa ba. Ina kira ga Sojojin Najeriya da sauran jami'an tsaro da su ƙara tabbatar da tsaro a wannan hanya domin hana irin wannan harin a nan gaba.''
Harin ya sake jaddada matsanancin kalubalen tsaro da ake fuskanta a yankin Arewa maso Gabas, yana kuma ƙara nuna bukatar ƙarfafa matakan yaki da ta'addanci domin kare rayuka da dukiyoyin al'umma.