Fargabar rinchabewar rikicin Sudan ta Kudu
March 27, 2025Wannan lamari dai ya sanya fargabar rushewar yarjejeniyar zaman lafiyar da aka cimma a 2018 da kuma barazanar jefa ƙasar cikin yaƙin basasa.
An tsare matamakin shugaban ƙasar Sudan ta Kudu na farko Riek Machar, wanda ya daɗe a matsayin abokin hamayyar Shugaba Salva Kiir, a gida, in ji jam'iyyarsa.
Wani jerin gwanon jami'an tsaro ƙarƙashin jagorancin ministan tsaro in ji jam’iyyar SPLM
"A iya cewa, Dr Machar yana a tsare a gidansa, amma jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin ɗauke shi daga farko," in ji Reath Muoch Tang, shugaban kwamitin harkokin wajen jam'iyyar.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta jima tana gargaɗi cewa Sudan ta Kudu na dab da komawa yaƙin basasa bayan rashin jituwa tsakanin Machar da shugaban ƙasar ta ƙara tsanani.
Shugabannin biyu sun cimma yarjejeniya a watan Agutsan shekarar 2018, wadda ta kawo ƙarshen yaƙin basasa na shekaru biyar wanda ya kashe mutane kusan 400,000
Amma cikin shekaru bakwai da suka wuce dangantaka tsakaninsu tana ƙara tsami cikin tashin hankalin ƙabilanci da kuma arangama da ake samu lokaci zuwa lokaci.